HASSANA DA HUSSAINA 189 & 190πŸ’œπŸ’œπŸ’œπŸ’›

Daren da farhana ta sanar da adil cewa tana dauke da juna biyu ,sukayi ceceku kuce,yace mata seta zubar dashi ita kuma ta are ta yafe da cewa bazata zubarda shi ba,bayan fitar adil daga gidan farhana be taka birki ko ina ba se gida ,inda ya tarar da mahaifiyar sa zaune akan sofa tana kallan india drama akan zeetv “qubulhe”se murmushi take abunta,ko sallama beyi ba  ya zarce zuwa dakinsa,taji alamun shigowarsa amma tayi dai da duniya kaman batasan da shi ba,bayan shigarsa daki safa da marwa ya hau yi,saboda besan ta inda ze fara ba,duk inda ransa yake ya bace,fuskansa ko alamun daria babu….daren kwatakwata adil be runtsa ba…farhana kuwa bayan fitar adil daki ta nufa ta fada bandaki tayi wanka,tasa sleeping gown dinta fara kana ganin jikinta,tayi kwanciyarta harda munshari,dan gaba daya abunda ya fada be tabata ba ko daga nan zuwa cen se qarfin guiwar da ta qara samu naqin zubarda cikin…

****few month ltr***farhana da adil suka shafi wata hudu ko waya babu,kowa ya fita batun wani,farhana se lelen cikinta take har ya fara fitowa ya mata kyau sosai,kyaunta ya qara fitowa,ta qara lafiya.hankalinta kwance amma tunda ta samu ciki bata cika zama a calfonia ba idan bata uk tana us.baturiya makwabciyarta kuwa tayi tafiya zuwa china dama yar cen ce,duk abunda ke faru da farhana batada masaniya amma cen baa rasa ba suna waya da farhana,akwana a tashi ba wuya awurin Allah cikin farhana ya qara fitowa …..tana zaune a fallo kan sofa ta dora bowl din popcorn akan cikinta,se ci take tana lumsar ido,cen naga tayi saurin dora hannunta akan gefen cikinta,cikin murya yar qarama tace com on hero,kada ka wahalda mummy fah,cen se naga ta gyara kwanciyar taci gaba da sha’aninta,misalin qarfe biyu na rana na hango farhana ta fito daga dakinta ,sanye take cikin wata doguwar riga baqa mai silky hand ta zubo gashin kanta har gadon baya,ta qara kyau da sheki…..kofar dakin ta janyo sannan ta qaraso zuwa fallo tako take kaman batasan taka qasa,qaraurawar gidanta aka danno,tsaki tayi sannan tace wanene kuma?qarasawa tayi ,tana bude kofan ta hango qawarta asma’u jega,ido ta fiddo tace shegiya?rungume juna sukayi,sannan suka qaraso cikin gidan.fallo suka zauna nan suka hau fira,asma’u tace ina  megidan naki?murmushi farhana tayi tace nayi maki kama da mai aure ne?asma’u tace toh ina zaki da uban ciki haka?farhana tace kedai bari akwai gist a qasa,ranar qawayen farhana se zuwa suke,sun kai kusan su goma agidan,suka cika gidan se firar su suke,nan qawayen farhana suka takura mata da seta basu labarin yanda tayi aure basuda labari,farhana ta lumshe ido se hawaye ta fara zubarwa,hankalin su yayi mugun tashi sukayo ruuu kanta se lallashinta suke,nan ta kwashe komai tun daga farko ta gayamusu,sun tsinewa adil har babu adadi….

Agidan ta asma’u ta tare da yake farhana ita kadai ce ,yau cikinta haihuwa yau ko gobe,suna zaune da asmy a fallo,suna kallan news se aka nuno hoton adil da wata baturiya cewa sunyi aure,farhana tayi murmushi tace asmy kingani koh?asmy tayi shuru tace kada kidamu in sha Allahu bazai ci bulus ba,sati biyu da faruwar hakan qarfe uku na dare  nakuda ta kamata asmy ta kaita hospital amma ta kasa haihuwa da kanta,akamata cs dan bezo da rai ba,bayan ta samu sauqi ne ta qara neman adil,ta fara blackmailing dinshi nacewa ta haihu idan be aureta ba zata kai dan gidan su,bayan sun daidaita kaman ba abunda ya faru tasawa adil guba a drink yasha,bayan ya koma gida cikinsa ya dinga masa ciyo daran aka kai shi hospital,amma ya nemi alfarma cewa agayawa duniya cewa ya mutu,daga nan ne yabar garin calfonia ya koma uk da zama gaba daya da shi da iyalan sa,farhana kuwa daga lokacin ta zama tantiriya ,bata ganin girman kowa bata ragawa kowa,se abunda take so take,tafi qarfi mahaifanta. Harta kawo gidan sarki qamar wanda a sanadiyar hashim ta qara mallakar hankalin kanta.wannan shine takai taccen labarin relationship din adil mahaideen khaleeed da farhana justice ameenu…..

***MU DAWO LABARIN MU****

Bayan isar mr nd mrs mahaideen khaleed offishin dr james ya kwashe komai ya gayamasu,raziqa khaleed tace gaskiya wannan abun yana bani mamaki anya adil yana da hankali kuwa taya zebarta ciyo yayyita cinta amma ya kasa daukan kwawkwaran mataki akai,taya zaayi ace duk ta dauki ciki seya zube,dix ix impossible gaskiya da wata a qasa,mr khaleed shuru yayi yana saurarenta amma hankalin shi gaba daya baya kanta,hannu ya daga mata yace wait zaki tuna tsohuwar budurwar shi ?mrs khleed tace u mean to say raziqa?yace yes ofcourse ,shes related to dix,na tabbatar adil knows what is going on?mrs khleed ta dan fito da ido waje tace anya adil yasan inda take kuwa?tunda ya gayaman cewa auren dole aka mata shiyasa ya amince da soyayyar sumayya,kuma kasan cewa sumayya diyar qawar friend dina ce duk abunda ya sameta i will b hold responsible shiyasa tun  farko bangoyi bayan auren ba,mr khaleed yace yanzu dai abunda ya faru ya riga ya faru,muje mu ganta,dr james yana sauren su se ido ya zuba musu,murmushi yayi yace please take things easy shes getting much better please,she will be fine,mr nd mrs khaleed suka amsa mashi cikin sakin fuska sunji dadin yanda ya musu sosai,miqewa tsaye sukayi suka nufi waje busu taka birki ko ina ba se wani daki inda na hango wata santaleliyar yarinya kwance da drip ahannunta tana bacci,mrs khaleed ta girgiza kai saboda tausayi,gefen gadon ta zauna tana shafar kan yarinyar ahankali,mr khaleed yana bayanta ya dora hannayensa biyu akan kafadarta,sunjima ahaka sannan suka fito….bayan fitowar su busu taka birki ko ina ba se gida inda mrs khaleed ta dannawa adil kira ta mashi umurni da cewa tana buqatar shi a calfonia yau ta tsinke wayarta,misalin qarfe 10:pm ya iso calfonia se gida koda ya isa gidan mahaifansa na zaune a fallo,cikin hanzari ya nufosu ze rungume su mahaifiyarsa ta daga masa hannu cikin fushi tace don’t even think of dat,i didn’t no u were so stupid ,cikin rawar murya yace mu—–my tace don’t mummy me,i need to no everything dat happen between u nd farhana,from A to Z,hawaye ne zafafa suka dinga zubo masa daga idanuwansa,cikin tsawa mahaifinsa yace are u deaf,se da gidan ya amsa……..

Zubewa yayi a qasa agabansu,yanda suka ga yana kuka kaman qaramin yaro yasa mahaifiyarsa tace i no dama nasani,dama nasan baa banza sumayya ke ciki yana zubewa ba,i hope u didn’t use her nd dump her?cikin muryar kuka yace mummy i wish i only used her nd dump her ,i also abandonned my own child,lokaci daya suka miqe tsaye,kalima suka hau yi gaba dayan su, mrs khaleed tace was she pregnant?daga mata kai yayi alamar eh,ta juya ta dubi mr khaleed dake gefenta ya zuba musu ido se kallo yake,bece dasu uffan ba se komawa yayi ya zauna ya hade kafafuwansa da kansa,matarsa ta lumshe ido ta dora hannunta akan kafadarsa daga kansa yayi sama ,tace kayi hakuri daddyn adil we have no time for dix,murmushi yayi yace mezamuyi”AYYI DUK MUTUNEN DA ALLAH KEYIWA FADA KAWAI YA KOMA YA ZAUNA NE”adil yayi abunda koni da nake ubansa bantabayi ba ,ya kikesan nayi?dubansa ya maida kan adil da har yanzu kukan yake,yace adil tell me how it happens,mahaifiyarsa ta shafi gashin kansa tace my son go ahead,komawa tayi ta zauna,shuru yayi na yan mintuna sannan ya kwashe komai tun daga farkon haduwar har zuwa yanzu,mahaifinsa besan lokacinda ya daga hannu ya kashe shi biyar ba,nan ya hau dukansa kaman wani kayan wanki mahaifiyarsa ta kasa ko motsi saboda gaba daya jikinta yayi sanyi……kasa jure ganin ana dukansa tayi ,ta miqe tsaye da gudu ta haura sama,sheshshekan kukanta yasa mahaifinsa ya dakata daga dukansa yace kaji haushi ,kaji kunya,adil what have we done to deserve dix,were u out of ur mind,naji akwai kaddara amma meyasa kayi abandonning danka na cikinka,do u no where she is now?to hell with u,shima ficewansa yayi,duk inda duniya take yau bata yiwa adil dadi,yayi da ya sanin qyale farhana,yanzu ta ina ze fara nemanta?tambayoyi daban daban yake yiwa kansa,gaba daya matarsa bata fado masa arai ba saboda kwatakwata bata gabansa,tunda ya aureta da ita da babu duk dai,se yana da buqata da ita yake nufo qofar dakinta,amma kash data samu ciki seya zube,har adil ya fara zarginta da ita ke zubarda shi,saboda bata buqatar haihu.WACECE SUMAYYA?SUMAYYA HAIFAFFIYAR YAR MADINA CE,MAHAIFIYARTA DA MAHAIFIYAR ADIL ABOKANAN JUNA NE,MAHAIFIYAR ADIL TANA KIRAN SUMMAYYA DA MAMANTA DA YAKE TANA DA SUNAN MAMANTA,SUMAYYA TA NUNA TANA SON ADIL AMMA ADIL KO KALLO BATA ISHE SHI BA,MAHAIFIYARSA TA KASA MASA MAGANAR SUMAYYA SABODA TASAN BAYA SON KOWA SE FARHANA ITAMA KANTA HANKALINTA YAFI KWANCIYA AKAN FARHANA,SUMAYYA KADAI CE MACE GUN MAHAIFAN DUKA YAYUNTA MAZA NE SU UKU ITACE TA HUDUN SU,DUK SON DUNIYA YANA KANTA,DUK ABUNDA TASA A GABA SETA SAMU AMMA BANDA ADIL,MAHAIFIYAR SUMAYYA TAYIWA MRS KHALEED MAGANAR AMMA MRS KHALEED TA NUNA MATA CEWA YANA DA WATA,AKWANA A TASHI ADIL YA DAWO GIDA YA ARE YA YAFE DA BAYASON KOWA SE SUMAYYA,MAHAIFYAR TAYI MAMAKIN HAKAN SOSAI DA TA TAMBE SHI FARHANA SE YAKE CEWA AUREN DOLE AKA MATA SHIMA SHI YAKE SO,GANIN HAKAN YASA TA AMINCE DAYA AURI SUMAYYA,BAYAN AURENSA DA SUMAYYA DA SHEKARA DAYA TA SAMU CIKI ,TAJI DADI SOSAI AMMA ADIL BABU WADDA TAKE TUNO MASA DA ITA IRIN FARHANA,DUK CIKIN DA TA DAUKA YANA DA WATA BAKWAI YAKE BAREWA,ADIL YASAN BAKOMAI BANE SE HAQQIN FARHANA DA DANSA DAKE BINSA,HAKAN YASA ADIL YA KASA SAMUN NATSUWA KODA YAUSHE TUNANIN YAKE TA INA ZE FARA IDAN MAHAIFANSA SUKA GANO GASKIYAR LAMARINSA DA FARHANA,wata rana sumayya tazo calfonia ganin surukanta,zaune take a fallo tana shan diyan itatuwa se lumsar ido take,tana zaune da dan cikinta 7month,miqewa tayi tsaye sulbi yajata se zubewa tayi a qasa,bayan ankaita asibiti ne dr yake sanar masu da cewa cikinta ya zube sannan yanada wuya ta qara samun wani,hakan ya sosa musu rai sosai,amma adil yajidadin hakan da aka sanar da shi saboda yana tunanin wannan ze bashi damar dawowa da farhana cikin tarihin rayuwarsa amatsayin matarsa ta biyu.se ga hakan ta kasance…..

SHIN YA TAKE NE?CONCLUSION FEWSL PAGES TO GO MRS NOOR NOVEL

 

HASSANA DA HUSSAINA 187 & 188πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘


Kallo adil yabi farhana da shi daga kanta zuwa kafafunta dake sanye da takalma,saukowa yayi daga kan gado ya cire mata takalmanta da yake masu belt ne black masu tsini sosai,bayan ya cire mata takalman ya miqe tsaye ya kashe wutar dakin ya ficewansa,wani daki ya nufa dake kallan nata iri daya ne,bandaki ya nufa yayi wanka ya sanya kayan bacci riga da wando,gadonsa ya hau ya kwanta lamp dinda ke gefen gadon kawai yake kunnawa yana kashewa cen ya miqe tsaye ya dinga safa da marwa acikin dakin,idanuwansa sun rine sunyi jawur,kofar dakin sa kawai ya bude ya nufi dakin farhana,koda ya kunna wutan dakin riganta ta dan janye kadan zuwa hips dinta saboda yanayin kwancin da tayi,gadon ya hau,ya fara sarrafata yanda ransa keso,sumbatar ta yake ta ko ina kaman “zakin da ya jima yana nema abinci be samu ba”nan ya maida farhana cikakkiyar mace,dakinsa ya nufa ya koma ya kwanta,yau ba qaramar natsuwa ya samu ba,hankalinsa ya kwanta sosai,baccinsa kawai yake kaman wanda ya mutu…..

******6am****

Bayan farhana ta farka dakin ta hau da kallo,lullube taga kanta cikin wani silky bed sheet gold,idanuwanta suka cika da galla,yanayin da takejin jikinta ya tabbatar mata da cewa wani abu ya faru,kuma taga kayanta a qasa,bakomai ajikinta,kuka ta fashe da shi na fitar hankali,hannu ta dora akan kai wanda yasa tayi wata kuwar da ta tada adil daga bacci,da gudu ya nufo dakin,wurinta ya nufa ya hau lallashinta cikin kuka take fadin ka cuceni kaci amana,why adil?why?jikinsa yayi sanyi sosai saboda besan lokacinda ya aikata hakan ba,yana hulda da mata sosai amma be taba bacci da mace ba,farhana ta tafi da imaninsa nesa ba kusa ba,ya rasa ta ina ze fara ya rasa ya zeyi,ficewa yayi daga dakin cikin hanzari,da kyar farhana ta samu ta miqe daga inda take bandaki ta nufa tako take kaman me koyon tata,ta jima a bandakin sosai,bayan shigar ta bandakin adil ya shigo dauke da tray babba,da wata shopping bag ahannunsa,alamu yaji na zata fito yasa yabar dakin da gudu,bayan ta fito ta tarar da kayanda ya kawo,hannu tasa ta watse su a qasa komai seda ya fashe ,abinci ne ya kawo mata da tea,haka ta watsar da komai a qasa,daure take da silku bed sheet dinnan,farhana ta shafi kusan sati biyu bataci bata sha kullun cikin kuka take,gashi batasan pin dinda ake amfani da shi gurin budi kofar dakin,amma kullun se adil ya kawo mata abinci,amma bataci wani sa’in koda ze shigo tana bacci wani sa’in kuma tana bandaki,adil yayi daya sanin aikata abunda ya aikata,shima kanshi banda ruwan tea ba abunda yakesha,yau kwana biyu kenan idan ya shiga sede ya tarar da farhana kwance,abun ya fara bashi mamaki,rana ta uku da yaje bayan ya aje tray din ya nufi wurinta,hannunsa ya dora akan kanta,zafi jikinta yake dashi kaman wadda akasa a oven, hankali yayi mugun tashi,daukan yayi kaman baby ya nufi bandaki da ita,farhana se kallan shi saboda gaba daya ko farcenta bazata iya dagawa ba,nan yayi mata wanka da ruwan zafi,ya gasa mata jikinta ,ya dauko ta ya shiryata tsab cikin wata doguwar riga yellow mai dogon hannu,ya kwantar da ita akan sofar da ke dakin ya cire bed sheet din yasa wani silky one black,ya gyara dakin tsab,sannan ya daukota ya jinginata akan fillo,tea ya hado mata mai zafi da kyar ya samu tana sha ,har tayi rabi ,sannan ta koma ta kwanta ,rufeta yayi ya fice daga dakin,bayan fitar ya kira family doctor dinsu wato doctor james yazo ya dubata ya rubuta mata magunguna,adil ya siyosu,kullun setaci abinci tasha magani,amma adil be qarajin koda alif bane ya fito daga bakinta ba,abun yana matuqar quna masa rai,babu yanda ya iya haka yaci gaba da kula da farhana har tsawon wani lokaci….ranar adil yana kwance akan sofa baqa dake fallonsa,yanata latse latse awayansa,kiransa akayi wata baquwar number ce ta shigo bayan ya daga ya cenza harshe zuwa turanci,bayan ya dan jima yana sauraran abunda wanda ke kiran shi ke fadi se yace alright den on my way,wayan ya katse ya nufi dakin farhana,koda ya shiga tana zaune idanunta biyu,murmushj yayi yace my wifey am going out i have something agent to attend to but i won’t stay long,if u need anything d code of d door is **adil 56**bata cemasa uffan ba,qarasowa yayi cikin dakin ya sumbaceta akan goshi,tare da juyawa ya fice abunsa,jin alamar kukan motarsa yasa tayi saurin miqewa tsaye,ta nufi tagar dakin tana leqawa yana ficewa,bayan ficewarsa da gudu ta fito daga dakin zuwa harabar gidan mota daya ce a fake wata camry2015 fara tasha tintect,komawa tayi cikin gidan tun daga fallo taketa bude wardrobes dinda ke fallon key din motan take nema amma bata samu ba,hannu tasa abaki ta cije yatsanta,da gudu ta nufi dakinda yake kusa da inda ta zauna,dakin adil pin iri daya ta danna ya bude tana shiga taci karo da durowar kayansa tana budewa taga mukullin motar,bata tsaya wata ba ta dauki mukullin ta fito da gudu motan ta bude ta shiga bayan ta nufo gate din taga alamun security yake da shi,nan ta hau latsa numbers kala kala,cen ta danna *456**ya bude taka motan tayi ta fice gidan kaman zata fira asama,bata taka birki ko ina ba se gidanta ,bayan gidanta taje tayi parking motan,tana fitowa ta nufi wani gida dake kusa da ita ta kwansa,bayan anbude wata baturiya ce tsohuwa mai kyau,tana ganin farhana ta zaro ido tace are you okay angel?farhana ta qirqiro wani murmushi ,bayan ta ida shigowa gidan take bawa baturiyar labarin cewa birthdayparty na friend ditta taje tayi hakuri bata kirata ba,baturiyar tayi murmushi tace da farhana ta dauko mata mukullin gidanta?farhana tayi saurin girgiza kai tace da tsohuwar nan takesan ta dinga zama,tsohuwar taji dadi sosai,kan kafafuwanta farhana ta kwanta nan ta hau massaging kan farhana har bacci mai nauyi ya dauketa,fillon sofa ta dauko ta dora kan farhana akai ta nufi kicin dinta…..

SE YA KENAN?MRS NOOR’S NOVEL

πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—bayan dawowar adil gida moto park dinda ke gabansa ya nufa kwatakwata hankalinsa baya kan wanda da ka shigo se shi,yau ta kofar baya ya shigo gidan nasa,yana shiga yayi murmushi ya zauna kan sofar da ke fallon se murmushi yake,gyara zamansa yayi zuwa kwanciya kansa na kallan sili se nazari yake,cen ya miqe tsaye ya nufi kicin,nan ya hau  hadawa farhana girki irin nasu macroni da salad da tomatoes,onion da sauran abubuwan,bayan ya gama ya dora akan babban faranti,ya dora lemun kwali na orange daya da cup da ruwan gora ya nufi dakin farhana,bayan shigarsa bega kowa ba yayi murmushi tare da gyada kai,trayn ya dora akan ya ficewansa ,shi a tunaninsa tana bandaki,dakinsa ya nufa shima yayi wanka ,ya cenza kaya ko yanzu riga da wando ne farare,kan gadonsa ya hau ya kwanta,se juyi yake abunsa…….sede kash yau ransa gaba daya baya masa dadi ,jin kansa yake so lonely,murmushi yayi miqe ya koma dakin farhana har yanzu tsit,kan gadon ya koma ya kwanta yafi awa uku a kwance amma beji ko alamun ruwa ba,miqewa yayi ya nufi bandakin ya tura kofan ba kowa aciki,ido ya fiddo yace what?nan ya hau kiran sunan farhana,kaman ya haukace,har harabar gidan yake se yanzu ya ankaro da motarsa daya bata gidan,guwawunsa yakai qasa tare da sa hannu ya rufe baki,hawaye ne zafafa ke fitowa daga idanuwansa,cen yace but wait taya akayi tasan pin dina na gate?waya dauketa?tambayoyine kala kala yake tayiwa kansa?hannunsa yasa a aljihu ya dauko wayansa ya danna fary bae yanda ya mata saving kenan,kira amma bata daga ba,qarshe ma switchoff ake cemasa ransa yayi mugun soyawa,gaba daya yau itace rana mafi muni agareshi,motansa ya nufa ya fice daga gidan,be taka birki ko ina ba se gidansu inda mahaifansa suke,irin gate din gidansa amma still sunada gateman,bayan shigarsa sunan farhana ya hau kira,masu aikin gidan suka fito da gudu su uku ne,se kallo suka bishi da shi,sunan da yaci gaba da kira ne yasa mahaifiyarsa ta sauko daga gidan bene,tana sauko tace whats wrong adil?why are u shouting?lumshe ido yayi tare da dafe kai,kallo daya tayiwa masu aikinta suka fice da gudu,gurin danta ta nufo tana qaraso hannunsa ta riko suka nufi fallonta dake a sama,bayan sun qarasa ta zauna tare da zaunar da shi nan ta hau tambayarsa meya faru ne ta ganshi haka?ido ya fiddo yace you mean to say farhana is not here,fuska ta ya mutse tace ta gayamaka zata zo ne?nan ya qara firgicewa ganin danta yanasan yafi qarfinta ta rungume shi qamqam tana shafar bayansa,kuka yake kaman wani qaramin yaro yana fadin am sorry farhana i really regret please forgive me,mummynsa raziqa tayi ajiyan zuciya saboda ta tabbatar danta nasan farhana..AMMA MEYA MATA DA YAYI REGRETING? Tambayarda take yiwa kanta kenan😒😒😒😒😒😒😒

Gefen farhana kuwa daki na tarar da ita kwance tayi wanka ta cenza kaya zuwa wata doguwar riga baqa mai hannun vest,tayi kyau sosai amma idanuwanta sun kumbura sunyi jawur da ka ganta kasan kuka kawai ne aikin nata,kwance take kan lafiyayyen gadon ta ,ta rungume fillo,se hawaye take,ta rasa meyake mata dadi duniya?alamar anbude kofar dakinta ne yasa tayi saurin runtse ido,baturiyar nan ce ta shigo bata qaraso ba ganin taga farhana na bacci,kashe wutar dakin tayi ta fice tare da jan kofar dakin,bayan fitar ta farhana ta bude ido,hannu tasa qarqashin fillonta ta dauko wayanta iphone6+ ta kunna,tana kunna texts ne daga adil har babu adadi,amma ba wanda ta buda,baquwar number ce ta kirata ,batayi gardama ba ta daga,bayan ta daga taji muryan babba mace tace hello?jin muryan yasa farhana ta tabbatar da cewa mahaifiyar adil ce da sauri ta kashe wayan tasata flight mood,ta juya taci gaba da kukan nata.

Gefen mummyn adil kuwa wato raziqa bayan ta samu ta lallashi adil har bacci ya dauke shi,ta miqe tsaye ta sauko daga gidan benen zuwa fallonta da yake qasa,kan sofa ta zauna ta dora kafa daya akan daya,wayanta na rike da hannunta se nazari take,amma ta kasa fahimtar kome adil yayiwa farhana da yake ta sambatun cewa yayi regretting,cen se zuciyar ta ta raya mata da ta kira farhana taji komai,haka akayi kuwa dannawa farhana kira tayi tajita kashe,haka ta dinga kira har na tsawon wani lokaci,kiran qarshen da tayi yasa ta samu,bayan farhana ta daga wayan tace hello?amma taji tsit har aka tsinke wayan,tsaki taja kaman zata cire harshenta tace badai banida kudi ba,haka akayi kuwa koda ta duba batada enough kudi awaya,lumshe ido tayi tace Allah sarki ina fatan bazatayi tunanin wani abu na daban ba,miqewa tayi ta haura sama………batasan cewa farhana ta katse wayan da kanta ba inji ni mrs noorπŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜

******few month later****an shafi kusan wata uku farhana bata qara neman adil ba,sannan bata qara fitowa waje ba,gaba daya tarewa tayi agidan tsohuwar baturiyar da ke kusa da gidanta,ganin yanda farhana ta ya mutse watannin baya yasa baturiyar ta damu sosai saboda ta dauki farhana tamkar diyar da ta haifa da cikinta duk abunda zai tabata bataso.yau ranar ta kasance ranar laraba farhana da baturiyar suna zaune akan dinning suna breakfast,da ka ga cin abincin farhana kasan tanaci ne kawai amma bawai dan tana so ba,baturiyar tayi murmushi tace da farhana ,ta manta yau shopping day tana fatan zata rakata?farhana ta qirqiro murmushi na dole tace da matar meze hana,matar taji dadi sosai,haka akayi kuwa misalin qarfe bakwai bayan sallah magrib suka shirya tsab cikin qananun kaya riga da sket,se dan qaramin gyalenda farhana ta yafa baqi.koda baturiyar ta fito farhana harta jawo motarta,tana jiran fitowarta,bayan ta fito suka wuce busu taka birki ko ina ba se se wani park inda ake kira shopping day ranar sayayya kenan,akwai discount har babu adadi amma duk abunda kake nema bazaka rasa ba.bayan farhana ta samu guri tayi parking,se suka fito suka nufi kasuwan,da ka gansu zaka rantse uwa da diya ne saboda gaba daya farhana batada kama da mutan 9ja,bayan sun shiga gurin baturiyar da take tare da farhana ta hango wasu qawayenta,cen suka nufa,suna zuwa sukayi musabaha da junan su harda farhana,anan suka rabu da farhana,amma baturiya ta gayawa farhana koda bata ganta ba kada ta damu ta koma gida kawai,farhana tayi naam da hakan.kowa se sayayya yake abunsa.

Sunfi minti talatin acikin park din,farhana se yawo take a kasuwan,ta rasa inda zata tsaya,wurin motarta farhana ta koma tayi tsaye ta zuba wani uban tagumi,jingine take a motan se kallan motoci take da yake akwai dan jayawa daga parking space zuwa inda ake sayayya,wata hadaddiyar mota ce na hango ta shigo faratas,bayan tayi parking,wasu manyan matane suka fito au biyu,cikin dogayen riguna na material,sun yafa gyale baqi ko wace rike take da purse,qarasawa nayi gurin wazan gani?raziqa mahaideen khalid ce wato mummyn adil tare da qawarta “shaya”sunyi kyau har sun gaji.cikin kasuwar suka nufa cikin iko da kasaita suke tafiya har suka isa cikin kasuwan, bayan sun shige abunsu,naga motan a slow take har yanzu kenan kawosu akayi,bayan yan mintuna naga anbude gambun motan,kafa daya aka fara takowa awaje,sannan aka kashe motan aka fito tun daga qasa na fara kallan koma wanene saboda haduwar da yayi koda nakai kaina a sama se naga adil mahaideen khaleed,ido na fiddo,fuskan shi ko annuri babu.tsaye yayi yana qara yiwa gurin kallo,kaman anyi da shi daya juyo zuwa hannunsa na dama ,yana juyowa ya hango wata jingine a mota ga duk kan alamu hankalinta baya jikinta,tako yayi zuwa wurinta yana zuwa yaga farhana,kasa ko motsi yayi saboda yau ba qaramin farin ciki yake ciki ba,cikin hanzari ya qaraso gab da ita hannu ya dora mata akan kafada tayi mugun juyowa a tsorace ido biyu sukayi da adil,tana ganin shi ta wani juyawa zata gudu ya riko ta ya hadeta da motanta,cumuimuye fuskanta tayi guri daya ,adil kuwa se kallanta yake,cikin harshen turanci tace “get ur fricky hands off me okay”murmushi yayi yace am sorry farhana try to understand me it wasn’t intentionally,i love u so much nd am ready to marry you,jin hakan yasa zuciyarta tayi sanyi,amma ta nuna masa batasan shi ,batasan mai son shi,zata qara furta wata kalma ya saka bakin shi a nataπŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Daga nan ne adil mahaideen khalid da farhana justice Aminu suka fara rayuwa irin ta ma’aurata,gaba daya ta tare gidan shi,soyayya sukeci abunsu kaman bazaa mutu ba.har ta samu ciki ,yace seta zubar da shi tace aaaah.ita tayi renon cikinta har yakai wata tara ,amma ta kasa haihuwa da kanta dole aka mata c.s amma dan nata bezo da rai ba.daga nan ta qudurta seta kashe adil mahaideen khaleed,haka akayi kuwa amma abun tambaya anan shine anya adil ya mutu?meyasa mahaifansa suka goyi bayan aurensa bayan sunsan farhana ce yake tare da ita?wacece mahaifiyarta dake kwance a hospital?tau fah ……

CONCLUSION ON D WAY…….MRS NOOR’S NOVEL 10:45AM❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀UMMAN MAHAIDEEEN…….


HASSANA DA HUSSAINA 185 & 186πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žβ€

Ajiyan zuciya abban farhana yayi,har ya juya ze ficewansa nabil ya riko hannunsa tare da girgiza masa kai,lumshe ido yayi tare da qara kallan nabil,umman farhana da farhana kuwa kuka suke sosai,sun rungume junan su,tako abban farhana yayi zuwa gurin su cikin hanzari umman farhana ta janye farhana zuwa bayanta ,hannu ta daga mashi,cikin rawar murya tace kada dai kaceman kayi regretting?shes now my daughter let her be in my control for a while,bazan iya jure ganin ka dorata akan turbar da bata dace ba,saboda farko nayi babban kuskure na kawo ido na

zuba muku,but dix time around am not going to take dix,juyawa tayi ta jawo hannun farhana zasu fice,mahaifinta ya miqo mata hannu,ganin hakan yasa farhana ta riko hannunsa itama,jin farhana ta tsaya chak yasa mahaifiyarta tayi mugun juyawa ganin farhana ta riko hannun mahaifinta tana zubarda hawaye yasa mahaifiyarta ta tsaya chak tare da sakin hannunta,rungume mahaifinta tayi,mahaifiyarta ta juya ta basu baya harga Allah taji dadi amma ta nuna musu ko ajikinta,nabil yayi murmushi tare da girgiza kai ,tako yayi zuwa wurin mahaifiyar farhana,gabanta ya tsaya,yayi nisa sannan yace haba mummy kiyi hakuri,ki kuma yiwa Allah godiya daya nuna maki rana irin wannan,u re so lucky to witness dix day,please forgive him please,duba kiga yanda suke a yanxu d family is incomplete without u,please complete dix lovely family,jin kalaman nabil sun kashe mata jiki yasa ta qara zubarda hawaye,tako tayi zuwa wurin farhana da daddynta ta rungume su,farhana taji dadi sosai,mahaifinta ya rungume matarsa da yarsa cikin so da kaunar juna ,nabil kuwa yau yafi kowa farin ciki saboda ya tabbatar Allah ne kawai ze hana ya auri farhana…………

Yau ranar assabar misalin qarfe bakwai na safe,mummy mashkura tana kwance akam lafiyayyan gadonta,se juyi take,sanye take cikin jallabiya baqa,zaune ta tashi tare da zuba wani uban tagumi,juyawa tayi zuwa hannunta na hagu ta dauko fillo ta dora kan kafafunta seta dora hannayenta sama,knocking kofar dakinta ne da ta jiyo anayi yasa ta sauko ta nufo kofan,mukulli ta murda seta bude dakin ,basma ce tsaye bakin kofar dakin,ido ta zubawa ummanta sannan tayi murmushi tace mummy lafiya kuwa?mummy mashkura ta juya tare da barin kofar dakin bude,basma na tsaye abakin kofar dakin se kallo ta bita da shi,kan gado mummy mashkura ta dawo ta zauna,basma ta qaraso ciki tare da rufe kofar dakin gab da mahaifiyarta tazo ta zauna,tayi nisa tace mummy whats wrong?mummy mashkura tayi murmushi ta shafa fuskan basma sannan tace bakomai my angel banajin jikine yau,basma ta marairaice fuska tare da langabar dakai tace mummy sannu ki kwanta ki huta,mummy mashkura ta lumshe ido ta koma ta kwanta,basma ta miqe tsaye ta janyo silky bedsheet na rufa ta rufeta da shi,sannan ta fice daga dakin kallo mummy mashkura ta bita da shi harta fice,nisa tayi sannan tace lafiyana yau kuwa?gaba daya raina bayaman dadi,nayita kiran hashim baya picking calls dina,hassana ma haka whats going on ne?jikina yana bani something is wrong somewhere………

Gefen su nabil kuwa bayan yan mintuna suka saki juna,farhana takai guwawunta qasa ta nemi gafarar mahaifinta ,mahaifinta yayi farin cikin hakan sosai,mahaifanta sunyiwa nabil godiya har babu adadi,sunsa masa albarka tare da bashi farhana halak malak,ranar nabil ba qaramin dadi yaji ba,bayan mahaifiyar farhana ta gama yiwa mahaifin farhana wato megidanta bayanin komai ya nuna rashin jindadinsa na tafiya ta barshi cikin kunci da damuwa,ta bashi hakuri,yanzu ne suka dora niyar yin rayuwa irin ta addinin musulunci ,yanzu ne suka dora niyar yin rayuwa kaman yanda Allah ya ce,farhana taji dadi sosai….nabil ya jima agidan sosai sannan farhana ta masa rakiya zuwa harabar gida inda mota daya ce ta tsaya jiran shi dayan ta wuce bayan ta kawo su,nabil yayi murmushi ya tsaya chak wurin wata corridor ta gidan su farhana before ka ida fitowa harabar gidan,juyawa yayi ya dubi farhana cikin ido,ahankali ya matso da kansa zuwa fuskanta ja take da baya da baya harta kai gurin bango,ta juya zata gudu yasa hannu ya tareta,tsayawa tayi chak kanta a qasa,nabil kuwa se kallanta yake,murmushi yayi yace yaushe kikesan muyi aure?cikin hanzari ta daga kanta sama ta kalle shi,gira yaja mata,batace da shi qala ba,yace tau gimbiya tinda kyaleni kikayi kije kisa ranar da kikesan muyi aure koma yaushe ne ashirye nake,sannan ya saukar da hannunsa daga bangon,ya daga fuskanta sama ya sumbaceta akan goshi,lumshe ido tayi saboda wata natsuwa taji ta qara shigota,da gudu ta koma cikin gida,murmushi nabil yayi tare da girgiza kai,qarasawa yayi zuwa harabar gidan da kansa……..

Cen na hango wata mata sanye da leshi purple mai ratsen pink,ta yafa wani mayafi pink,riga da sket dinkin ya zaunu ajikinta,safa da marwa kawai takeyi,rike take da mukullin mota da waya iphone6 a hannunta koda na qaraso kusa senaga wata balarabiya,banyi qoqarin mata magana ba saboda bangane ta ba,fara ce tas,doguwa,ga hanci har baka,ga idanu barakalla baa cewa komai se ma sha Allahu,inda ba mutun bace da nace hurul-ayn ce,cen na hango wani bature ya fito cikin zanzaro wando baqi riga fara mai dogon hannu da ka ganshi kaga babban mutun,yana fitowa yayi murmushi wurin matar ya nufa ya sumbace rungume juna sukayi,sannan yayi nisa yana rungume da ita yace mata lafiya yaganta awannan lokacin?zame jikinta tayi daga nashi tace doctor james ya kirata yake gayamata cewa ciwon  mamanta ya tashi,yace kina nufin sumayya matar adil?tace eh,cikin harshen turanci ta masa magana,lumshe ido yayi tare dasa hannu ya shafi fuskanta,yace haba adil yana me ?wai meyake damunsa ne?nisa yayi yace wannan ba problem bane ,ta bari suje asibitin yanzu kawai,bata masa gardama ba suka fito daga wurin.company ne na sayarda motoci ,wurin tsit ko hayaniyar mutane babu,kowa yana gefen aikinsa,se sanyin ac ke tashi,bayan fitowar su basu taka birki ko ina ba se  babban hospital dinda ke calfonia inda family doctor dinsu hassana yake,wani offishi suka shiga suna shigo doctor james ya miqe tsaye tare da miqawa mijin nata hannu da su gaisa ,bayan sun gaisa ya basu umurni dasu zauna,murmushi doctor james yayi sannan yace your welcome mrs mahaidin,murmushi tayi tace thank u dr james……..

SU WAYE WADANNAN MR ND MRS MAHAIDIN?πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žMRS NOOR’S NOVEL


  Tau fah mr nd mrs mahaideen khalid kenan wannan shine cikakken sunan su,suna zaune  ne a cikin garin kaduna,sunyi rayuwa da komai acen ,bayan sunyi aure ne suka dawo calfonia da zama,anan sukayi rayuwar su,anan mahaideen khalid ya zama shahararren mai kudi a calfonia ,bayan shekara goma da auren su Allah be taba bawa matar shi koda miscarriage bane,duk wannan be tayar masu da hankali ba ,sunje qasashe da dama amma ina shuruu,bayan shekara goma sha biyar ta samu ciki,ranar mahaideen khalid yayi kyauta da dukiya har babu adadi,yayi sadaka,har babu adadi saboda ko ajikinsa,lelen matar sa kawai yake wato RAZIQA mahaideen khaleed ,daran da nakuda ta taso mata ta haihu ta haifi baby boy wanda aka yiwa suna da Adil mahaideen khalid duk wani son duniya yana kan yaron ,sun bashi tarbiya ta musamman saboda bama a calfonia yayi karatu ba madina suka izashi gurin karatu,ya samu gata sosai ,adil khalid fari ne dogo,ga hanci har baka,ga idanu sexy eyes kaman yamajin bacci,ga bakinsa pink dan tsito,da ka ganshi kaga balarabe,ayyi nihin kakanninsa mutanen egyt ne,mahaifinsa ba dan 9ja bane kawai zama ne ya kawo mahaifansa har ya hadu da mahaifiyar adil,ainihin mahaifiyar adil yar adamawa ce,itama zama ne ya kawo mahaifanta agarin kaduna,adil shi kadai ne ga mahaifan shi,mata suna san shi sosai saboda kyaun sa da kudin mahaifansa,wata rana ya fita shan iska a park dake calfonia yana zaune a bakin ruwa se kallan ruwan yake,cen ya hango wata na qoqarin nitsewa a ruwan,ya miqe tsaye da gudu ya shiga ruwan ya kamota,daukota yayi kaman wata baby,ya kwantar da ita kan carfet dinshi daya shimfida,ga duk kan alamu ruwa sun shigeta sosai danko motsi batayi,bakinsa yasa anata ya hura mata iska,se tashi tayi a firgice,tana lumsar ido,adil kuwa se kallanta yake,farhana ce cikin swimming custom,kana ganin jikinta ,idan ka ganta zaka rantse ba musulma bace,adil kuwa ko kyabtawa ba yayi  se kallan farhana yake dake qoqarin maida numfashinta,bayan ta dawo hayyacinta ta dubi gabanta ido biyu sukayi da adil,harara ta banka masa ta miqe tsaye ta ficewanta,shi kuwa imani ya masa yawa,ya zaayi ya temaketa ta kasa ce masa thank you?se harara zata banka masa,harta fice kallonta yake,murmushi yayi ya koma ya zauna,yaci gaba da kallon ruwan,farhana kuwa bayan ta fice wurin da ta aje kayanta ta nufa towel qarami ta daura,sannan ta dauki jakanta ta ficewanta……..

Bayan sati biyu da faruwar hakan adil ya kasa bacci,kullun se tunanin yanda ta banka masa harara take,abun ya birge shi sosai,ga shi ko sunanta be sani ba,kwance yake kan lafiyayyan gadon shi se juyi yake yana murmushi,miqewa yayi ya nufi bandakinsa dake cikin dakin,wanka yayo,yaci ado cikin wasu qananun kaya,riga da wando black,ya feshe jikinsa da turaruka masu qamshin gaske,yayi kyau sosai,ya saka agogonsa rolex baqi,komai black yayi,mukullin motarsa ya dauka dake kan dressing mirro din ,ya ficewansa daga dakin tare da janyo kofar dakin,wata hadaddiyar mercendez benz ya shiga fara mai tintect baqi,sanyin ac ne kawai ke tashi tare da qamshi be taka birki ko ina ba se park inda ya hadu da farhana,gurin ruwan ya zarce ko yau,cen ya hango wata santaleliyar yarinya zaune cikin qananun kaya riga da wando,riga pink wando baqi ,tayi fakin gashin kanta guri daya da rubom pink kan carfet baqi take zaune ,daga gefenta na dama akwai lemun kwali da cup da wayanta,da ka ganta kaga yar hutu ce,murmushi yayi ya qaraso yana zuwa ya cire takalmansa kan carfet din ya zauna gab da yarinyar mugun juyowa tayi ,ashe farhana ce,bata ce masa uffan ba bancin sunyi four eyes se juyawa da tayi taci gaba da abunda take ,murmushi kawai adil keyi yana qara mata wani kallo mai tafiya da hankalin mai tunane,farhana kuwa ko ajikinta saboda gaba daya be dameta ba,gyaran murya yayi sannan yace am adil mahaideen khaleed but u can call me adil khaleed nd u?ta jima bata ce masa uffan ba se cen tace am farhama Aminu ba tare da ta juyowa,yace what a beautiful name,are u from arabian?ta juyo cikin iko da kasaita irin na yaryan manya tace no am a nigerian,nan suka hau introducing junansu,amma adil be yadda da cewa farhana yar nigeria bace saboda kwatakwata batada kama da su,nan suka hau yin firar calfonia,farhana tace meyasa yakesan zuwa nan?adil yayi murmushi yace kawai gurin yana kwantar masa da hankali yana kuma bashi natsuwa ita fah?farhana tayi ajiyan zuciya tace kawai yana tuna mata da wani abun qaunarta wanda duniya bata hada kowa da shi ba,wanda koda yaushe tana tunanin ze dawo zuwa gareta,adil yace wanene wannan?farhana tayi murmushi tace his name is nabil he means d world to meπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žadil ya lumshe ido saboda har ga Allah beji dadi ba,amma be nuna mata ba se murmushin da yayi  ,ya miqo mata hannu yace can we be friends?cikin ido suke kallan juna sannan ta miqo masa nata tace yeah ,a ranar farhana se bayan isha’i ta koma gida abunda bata saba yi ba dadewar farhana a park qarfe shida,ranar bata zo da mota ba dan haka ranar adil ya zaga da ita cikin garin calfonia sukayo shoppings kaman wadanda suka jima tare,ranar farhana ba qaramin farin ciki ta shiga ba,har gida adil yakai farhana sannan ya shigar mata da kayanta sukayi seda safe ya ficewansa….wasa wasa soyayyar mai qarfi ta shiga tsakanin su,koda yaushe suna tare mahaifan adil sun san farhana sosai kuma suna son zamanta da dansu saboda ba qaramin farin ciki ya shiga ba haduwar sa da farhana,burin mahaifansa kuwa daya ne su ganshi cikin walwala da jindadi😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍

Wata rana adil ya dauki farhana zuwa partyn wani abokinsa ,turawa ne kawai awurin,saboda ko banbanta diyan musulmai baxaka iya ba saboda dukan su shigar banza ce sukayi,farhana ce kawai sanye da doguwar riga red har qasa mai dogon hannu,ta daura black veil wanda ta fito da gashin kanta har gadon baya,tayi kyau sosai,adil kuwa cikin coat yake fara,duk inda suka wuce se an kalle su,saboda ba qaramin matching sukayi ba da juna,adil ya samowa farhana vip ta zauna wurin tsit se qamshi da kwalliyar gurin kawai kake gani,aka jera mata drink daban daban,nan farhana ta shan drinks dinta seda ta shanye su duka,tayi tatil,se bacci da yayi awon gaba da ita,bayan awa daya adil ya dawo koda ya shigo dakin ya tarar da farhana kwance akan sofa,gaba daya ta shanye kwalaben drinks dinda aka kawo,da gudu ya nufi wurinta ya hau girgizata amma yaji shuru bacci ne mai qarfi ya dauketa,qanqarar da aka kawo cikin wani silver jug yasa hannu ya dauko daya yau hau shafawa farhana afuska amma seka rantse ba abunda ake mata,ganin hakan ya adil ya razana ya dauki farhana kaman wata baby zuwa mota,be taka birki ko ina ba se gidanta,ya nemi mukullin gidan ya rasa gashi besan inda take ajiya ba,nan ya yanke hukunci kaita gidansa ,be taka birki ko ina se gidan sa ,wani abu kawai ya latsa ajikin motarsa gate din ya bude,bayan ya shiga ciki gate din ya rufe kansa,tau fah aljanna duniya inji ni mrs noor,fakin space ya nufa,bayan ya faka ya dauko farhana ya shiga cikin gidan ,gidan babbane sosai komai na gidan golden ne,kallo nabi gidan da shi,ga duk kan alamu komai na gidan da computer yake aiki saboda duk inda keda kofa sede ya danna wasu numbers dakin ya bude,wani hadadden daki yakai farhana,gadon ba qarya ya hadu,se juyi gadon keyi bayan ya dora farhana akai ya danna wani abu akan gadon,ya tsaya chak guri daya,shafar kan farhana yake ahankali,ita kuwa bacci ne acikinta sosai……

MRS NOORS NOVELπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žHISTORY OF ADIL MAHAIDEEN ND FARHANA AMEENU…..7:30pm

HASSANA DA HUSSAINA 183 & 184πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

******NIGERIA*****Mummy mashkura ce zaune cikin wani hadadden fallo,sanye take cikin riga da zane na leshi,ta daura dankwali,tayi kyau sosai se kamshi take,gefen hannunta na dama kuwa wayanta ce a aje qirar iphone 6+,kallo take tana kallan arewa24  film din wasan hausa ne sukeyi mai suna huzna ko husna,se sanyin ac ke tashi kaman england saboda sanyin da ke tashi a fallon,kofar fallon ce da aka turo yasa tayi saurin maida dubanta zuwa kofan,basma ce ta shigo tare da zeezee,riga da sket ne ajikin su na qananun kaya,black nd red sukayi se fakin gashin kansu da sukayi da rubom black sunyi kyau sosai,da sallama suka shigo,mummy mashkura ta amsa musu cikin sakin fuska,fuskanta dauke da murmushi,zama sukayi gefenta suka bata fuska,ba wanda yace da ita uffan,ganin yanda suka shigo mata ba wasa bare sakin fuska yasa tayi gyaran murya tace lafiya kuwa yan matan mama?zeezee cikin muryan shagwaba tace mummy kinji aunty hidaya koh?mummy mashkura tace meya faru?basma tace wai ita ala dole kaya iri daya zamu saka da yan gefen ango,kuma mummy kinsan mun gayamaki dubai zamu mu siyo material a mana dinki kaman yanda aka mana a bikin yaya hashim,mummy mashkura tayi murmushi ta shafa kan basma dake gab da ita tace ya isa hakanan,ina ita hidayan take?zeezee zatayi magana,seji sukayi ance ganinan ,hidaya ce ta shigo cikin riga da sket na atamfa red,tayi kyau sosai,ta fara qamshin amarci😜😜😜😜,mummy mashkura ce maza qaraso nan ki rageman tsawon taya zaki ce yan matan mama su saka kaya iri daya da yan gefen ango,kina ganin yan gefen daman mama da baba kina son ki raina su,dariya ta tuntsire da ita,ta zaro ido ta dafe kirji tare da cewa na isa,ayyi mummy kinsan inbasu ayyi ba biki,for dat matter bikin big aunty dinau gaba daya,wasa nake ,dama shine ku ka baroni acen ku ka dawowan ku,baki suka murguda mata su biyu,ba wanda ya tanka mata cikin su,ganin duk sunyi kaman basajin su yasa mummy mashkura ce kuje kuyi browsing irin kayanda kukesan ku saka,da kuma inda kukesan amaku dinkin se kuzo muyi deciding yanda zaayi ,duka lokaci daya suka juyo zuwa mummy mashkura kai ta gyada musu rungumeta sukayi sunata jindadi,bayan sun gama suka juya zasu fice daga fallon,hidaya ta marairaice musu tace nifa?suka juyo suka kalli mummy mashkura ido kawai ta lumshe musu,suka rungume hidaya,tace am sorry i was just kidding,basma tace warning,suka fice daga fallon,bayan fitar su hidaya ta dawo gab da mummy mashkura ta zauna……..

Murmushi mummy mashkura tayi tace ya akayi?hidaya tace dama mummy nayi magana da tara makeover taceman each makeup on d 4 event zasu kama 5point something,mummy mashkura ta gyara zamanta tace toooh what about d dresser?hidaya tace kathyanthony ce dama so wannan ba problem bane nayi magana da ita,mummy mashkura tace okay then duk anyi mai wuyan dama problem din dresses din ne,but wait wai kuwa kinyi waya da hassana kuwa?hidaya tace no na kira dazu bata daga ba,tace yarima fah?tace nayi waya da shi yaceman idan ya koma ze kirani,mummy mashkura tace gaskiya da zaifi sauki saboda kayan da ta saka ran kamu sun man kyau dinkin yayi kyau sosai,but make sure kunyi waya da ita ,se ki gayamata abubuwanda akayi kinga idan zaa qara ko zaa rage ne se na sani tun yanzu,hidaya tace alright den,wayan mummy mashkura ce tayi qara ,mai martaba ne ke kan screen dinta,sarki qamar ne ke kiranta,hidaya na ganin hakan tayi murmushi tace bari naje mummy,miqewa tayi ta fice abunta,mummy mashkura tayi murmushi tare da daga wayan…

Bayan fitar hidaya dakinta ta nufa,mayafinta ta dauko kan gado fari na R & S  ,se ta nufi durowar gadon ta dauko purse qarama da mukullin mota,ta kalmanta ta saka flat shoes farare,ta fito daga dakin,bayan fitowarta wayanta tayi qara,tsayawa tayi chak koda ta duba se taga adnan ne ke kiranta,murmushi tayi tace hello,bayan sun gama gaisawa,tace alright toh ganinan zuwa,seta katse wayan,harabar gidan ta nufa inda ake faka motocin gidan,fadawa da masu aiki se gaisuwa suke kaiwa zuwa ga gimbiya  hidaya,wurin wata hadaddiyar mota naga ta nufa wato mercedens benza fara wadda tasha tintect har ba iyaka number motar gimbiya h,ga duk kan  alamu motarta ce,bayan ta shiga motanta gefen mai tuqi,gefen mai zaman banza ta dora wayanta da kuma purse dinta,wangame mata gate din gidan akayi ta fice abunta kaman zata fira sama,kidan gwanja ne ke tashi a motan ta kujerar tsakar gida binshi take yana rera waqan seka rantse tare suka hada baitukan ,gata ma sha Allah ba qarya yai hidaya tayi kyau cikin ba wata doguwar kwalliya tayi ba,daga powder se lipgloss dinda ta dan aza saman lips dinta…..

Bangaren su adnan kuwa,se shirye shiryen bikin sa yake,baya nan baya cen,itama kanta hajia nafisa baa barta abaya ba mahaifiyarsa kenan,danta daya tilo zeyi auri,dan haka so take bikin danta ya zama topic of d year 2017,saboda bikin adnan ta aje aikin ta gefe,komai itace ,ta shiga nan ta fita cen,gaba daya yan uwansa kowa se murna yake saboda abunda suka jima suna jira kenan,shine suji auren adnan,har yanzu adnan be bari kowa yaga matarsa ba,a fallo na tarar da hajia nafisa zaune akan wata sofa mai kaman gado fara,kafa daya ta dora akan daya,kanta a qasa rike take da wani dan qaramin littafi da biro ahannunta se rubuce rubuce take abunta gaba daya attention dinta nakan littafin,se sanyin ac dinda ke tashi gami da qamshi,adnan ne ya shigo fallon tare da sallama sanye yake cikin kaftan brown dinkin zaria,se hula baqa da ya saka,se agogonsa rolex baqi ,yayi kyau sosai se kamshi yake abunsa,yana shigowa ya zauna gab da mahaifiyarsa murmushi yayi yace mummcy har yanzu baki gama ba?ba tare da ta dago kanta ta dube shi ba tace kaidai bari autan mama,kasan banasan asamu matsala ko kadan ce shiyasa kaga na daddage,murmushi yayi yace lallai mummy dagaske kike,ni zan fita zamu fita da hidaya ne,tace okay but a minute,tadan dauki lokaci tana rubutu shi kuwa se kallan ta yake,bayan ta gama ta rufe littafin ta dora shi akan table dinda ke gefenta nisa tayi tace son?yace naam mummy,tayi murmushi tace yaushe zaka kawoman hidaya ne?ko nima ina cikin mutanen da bazasuga matar ka bane?gashi har anfara shirye shiryen evrnt bansa daughter in-inlaw dina a ido ba,ido ya fiddo yace haba mummcy ayyi hidaya ba tawa bace taki ce baki daya,yaushe kikesan ki ganta?murmushi tayi tace today is okay,yayi shuru se cen yace angama queen mother yau zaki ganta,tayi murmushi tace i trust my son,rungumeta yayi ,sannan ya miqe yace ya fita tayi mashi adawo lafiya,bayan fitar shi tayi saukan zuciya mai qarfi tace Allah sarki dan baba,Allah ya baki zaman lafiya……

Bangaren su farhana kuwa,bayan saukar su kano,nabil yayi waya akazo aka dauke su da motoci guda biyu naji da fadi,busu taka birki ko ina ba se gidan su farhana,bayan an wangame masu gate din gidan suka shiga,bayan sun fito suka zarce se cikin gida farhana da nabil ne a gaba mahaifiyar farhana tana biye dasu baya,zaune suka tarar da shi a fallo yana karatun jarida,nabil ne yayi sallama,bayan ya daga kansa se sukayi ido biyu da nabil,miqewa yayi yana marhaban da zuwansa,musabaha sukayi bayan sun gaisa,har qasa farhana takai ta gaida shi ya amsa amma ba dan ya gane wacece ba?una sauraren naji shigowan mahaifiyar farhana amma naji shuru,bayan sun zauna,suka gaisa cikin girma da girmamawa,mahaifin farhana yace toh ma sha Allah,me zaa kawo maka?nabil yace aaah daddy bana buqatar komai,juyawa yayi ya maida dubansa zuwa farhana dake zaune akan one seater ta cumuimuye kanta guri daya kanta a qasa,yace daddy baka gane ta bane?mahaifin farhana yace ko alama bangane ta ba,nabil yace farhana?ahankali ta daga kanta sama idanuwanta sun cika da galla,jin nabil ya kira farhana yasa mahaifinta ya miqe tsaye tare da zaro ido,kallo farhana yake cike da mamaki ,kaman be taba ganinta ba,ita kuwa hawaye ne ke zubowa daga idanuwanta,mahaifinta ya juya ze ficewansa,na jiyo murya kan daga sama tana cewa :gwanda ka tsaya da komai ze maka sauqi,tsayawa yayi chak,ba tare da ya juyo ba saboda tabbas muryan matar shi ne ya jiyo wato mahaifiyar farhana,qarasowa tayi cikin fallon tana tako kaman batasan taka qasa,bayan kujeranda farhana take zaune ta  tsaya,tace tabbas abban farhana kwatakwata be dace ka gujeta yanzu ba,saboda koma menene kai ne sula,sannan tarbiyar kace,dama nagayamaka tabbas akwai lokacin nadama kuma gashi yazo,kuka ne farhana ta fashe dashi mai tsuma zuciya,nabil kuwa tsaye yayi kansa a qasa,jin muryan matarsa yasa ya juyo,ido biyu sukayi da ita,cikin rawar murya da rawar jiki ya daga hannunsa tare da nunata da yatsa yace umman farhana?murmushi tayi tace naam ban mutu ba ina raye,dama nasan hakan zata faru,dama nasan wata rana zaka guji diyarda ka haifa,zaka tuna lokacinda muke neman haihuwa kaman mu mutu,ka tuna lokacinda kake san Allah ya baka  haihu baka bacci koda yaushe kana rokon Allah ya baka haihu,haba abban farhana why?meyasa se yanzu zaka gujeta?miqewa farhana tayi tsaye ta zagaya zuwa mamanta ta rungumeta qamqam kuka take sosai……..

MRS NOOR’S NOVEL

   πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

             08064064020

πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

HASSANA DA HUSSAINA 181 & 182πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

Gefen mummyn ahlam da abban ahlam a daki na tarar da su yana rungume da ita ,se numfashi take maidawa saboda kukan da tayi,se shafar bayanta yake ahankali gaba daya jikinsa yayi sanyi,nisa yayi yace amma hamida ace kina facing irin wannan problem banida masaniya ,meyasa kike boyewa kanki damuwa ne?so kike ki jawa kanki ciyo ne?gyaran murya tayi muryanta a makure tace ba haka bane abban ahlam,ina tantama ne saboda banasan na tayar maka da hankali nd u re very busy dix days shiyasa,lumshe ido yayi yace duk da haka kinsan inda kin gayan tun farko da ba haka ba,dan Allah kidaina boyeman damuwar ki komai bayi na bane yin Allah ne but u re making things hard for yourself,kidaina kinji?daga masa kai tayi alamar eh batare da ta kalle shi ba,shi kuwa gaba daya tausayinta ya kama shi,shuru yayi ya daga kansa sama yana kallan silin,dama ya jingina bayansa akan fillo,kan hamida nakan kirjinsa,se lallashinta yake…

        πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

                        πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

                                                πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

                                           08064064020

                                                        πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

Bayan doctor ya kwashe labarin mummy hamida ya gayamusu se yayi ajiyan zuciya yace da hashim meyasa suke neman labarinta ne?murmushi yayi hashim ya kwashe komai ya gayamasa,doctor ya girgiza kai yace Allah mai yanda yaso,yanzu yanda zaaayi a gane cewa uwa da diya ne,shine a musu dna test,hashim yace how?doctor yace eh awon zesa agane komai,hashim zeyi magana se hassana ta shafa hannunsa dake kan kafadarta,tace doctor wannan ba masatala bace ,but zamu iya ganinta before mu wuce?doctor yace ofcourse why not,miqewa tayi tsaye hashim ya riko hannunta suka fito doctor na biye dasu abaya,busu taka birki ko ina ba se room 6,hashim ne ya tura kofar dakin tare da sallama ya shiga,koda ya shiga tana zaune ,ta jingina akan fillo tana latse latse akan ipad,doctor ne yayi magana da cewa mornin my patient ,kanta ta daga sama fuskanta dauke da murmushi tace mornin,ido biyu sukayi da hashim da hassana,kallo tabi hashim da shi nuna shi tayi da yatsa tace hashim right?hashim yayi murmushi yace yes ma’am,gaisawa sukayi da juna cikin sakin fuska,hassana harta kai zaune akan sofa dinda take dakin,hashim na gefen gadonta tsaye,tambayar su hanan tayi,yagaymata basa nan,taji dadin ganin hashim sosai kaman wanda ta jima tana jira,nan take tambayar hashim jikin matar sa?ya juya ya maida dubansa gun hassana dake kallan su,yace shes fine now ayyi itace wannan,mumy hamida ta sauko daga kan gado ta nufo wurin hassana,gab da ita ta zauna nan ta zauna tana shafar kanta ahankali tare da tambayar lafiyar ta da kuma ta yaranta?tace duk lafiya lau komai alhamdulillah nan ta hau yi musu addu’a cikin sakin fuska kaman wadanda suka jima da sanin juna,doctor  ya ficewansa bayan shigarsa tare dasu hashim…. mummy hamida tayi gyaran murya tace am so happy to see u all,sukace thank u ,sukayi shuru na dan lokaci,hassana ce ta katse shurun da cewa mummy we are here bcx of u,mummy hamida ta fiddo ido tace niii?hashim yace kwarai ma kuwa………

             πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

                              πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

             β€β€β€β€β€β€β€β€β€β€β€β€β€β€β€

Mummy hamida tace tau ina jinku dafatan  dai komai lfy lau?hassana tace alhamdulillah,wayan da ke hannunta ta danyi latse latse akanta nadan mintuna sannan ta nuno hoton family haka mama da baba da yara uku,koda na kusan to ta senaga familyn mummyn ahlam ne nunawa mummy hamida tayi tace wakika sani acikin su?karba tayi ta tsurawa hoton ido,jikinta ya dau rawa ,numfashinta yana fita sama sama,ganinta hakan yasa hashim da hassana duka suka tsorata,hassana ta dora hannunta akan kafadarta tadan girgizata tare da fadin mummy mummy!!!!!!kai mummyn hamida kafewa tayi guri daya tana kallan hoton, ta kasa cewa komai ,ta kasa cewa uhmmm bare huuuuummmmm,se lumshe ido suka ga tayi ta fada akan sofa ,cikin hanzari hassana ta hau girgizata amma taji shuru,hashim be tsaya wata ba da gudu ya fita,bayan yan mintuna ya shigo tare da doctor cikin hanzari,suna shigowa doctor ya hau dubata ,hassana na gefenta zaune,bayan ya gama ya maida dubansa kan hashim yace you have to excuse me,hashim beyi gardama ba ya riko hassana ta miqe da kyar suka fito waje,suna fitowa nurses sunfi uku suka shiga dakin cikin hanzari,hashim ya rungume hassana wadda jikinta gaba daya a sanyaye yake,murmushi tayi tare da lumshe ido ….

Gefen su mummyn ahlam kuwa yanda muka barsu haka na qara tarar da su,wannan karon bacci ne mai nauyi ya dauki hamida wato mummyn ahlam,abban ahlam se shafar kanta yake a hankali,ganin bacci mai nauyi ne ya dauketa yasa ya kwantar da ita akan fillo,ya sauko daga kan gado tare da lullubeta da silky blanket red,ya fice daga dakin,be taka birki ko ina ba se wani daki da naga ya shiga wanda ke kallan nasu,cen na hango ahlam kwance tana bacci kan lafiyayyan gadonta pink in color,komai na dakinta pink ne,se dayan bangaren da na hango danta namiji jariri cikin na shi gadon na babies yana baccin shi shima,hankalin su kwance,murmushi yayi tare da jawo kofar dakin….

                   πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

             08064064020 πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

                       πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Bayan fitowar doctor daga dakin mummyn hamida  bakin kofa ya tarar da hashim zaune hassana na jikin shi,gyaran muryan da yayi ne yasa suka maida dubansu kansa,murmushi yayi yace you look so tired,hassana tayi murmushi tare da lumshe ido,sannan yace da hashim see me in my office,office dinsa ya nufa suka biyo bayan shi,bayan sun zauna ya danyi shuru na yan mintuna sannan yace mr hashim am sorry about what happen,nd shes getting much better,sede tayi loosing memory dinta wanda zai dauki lokaci mai tsawo before tayi recalling wacece ita,amma idan san samu ne meze hana su maidata gidan yarinyar da suke tunanin diyarta ce ,shi ze dinga zuwa yana dubata suga ko zata iya tunawa,hassana tace haka ma zefi komai sauqi,hashim yace zasuyi hakan amma zasu koma suyi magana da ita hamida din,doctor yayi murmushi yace wannan ba matsala bace,hashim ya miqa masa hannu suka gaisa,sannan suka fito daga office dinsu,rakiya yayo masu har wurin motor park din suka wuce,ya koma cikin asibiti,kan hanyar su,hassana ta kwantar da seat din kujera ta kwanta,hannu ta dora akan cikinta,tare da lumshe ido,dubansa hashim ya maido kanta,hannunsa ya miqa zuwa cikinta shima ya shafa hannunta sannan yace sahiba lafiya?ido ta bude tare da murmushi tace lafiya lau,busu taka birki ko ina ba se gida,bayan shigar su gida ban daki hassana ta fada tayi wanka tare da dauro arwala,ta saka jallabiya baqa,sallaya ta shimfida ta saka hijab dinta brown dogo har qasa ta gabatar da sallah azzahar,bayan ta gama kan gado ta koma ta kwanta se bacci,hashim kuwa bayan isar su gida aka mashi waya,se cema hassana yayi zanje na dawo,be taka birki ko ina ba se companyn da ya taba zuwa a mashi hospital da botic,nan ya tarar da manager suka gaisa da junan su,murmushi manager yayi yace ansamu fili babba inda zaayi botic din wurin yana da mutane sosai sede zeyi tsada,hashim yace hospital fah?manager yace ayyi sun fara aiki akai,hashim yayi murmushi yace kudin ba matsala bane ze turomasa ta account,shi dai fatan shi ayyi masa komai wadattace ,managern yace wannan ba matsala bane.nan suka zarce zuwa offishin manager nan ya hau nunawa hashim plans din komai…….

❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀

                    ❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀

                                                 β€β€β€β€β€β€β€β€  

                                         08064064020

                                                       β€β€β€β€β€β€β€MRS NOOR’S NOVEL 

HASSANA DA HUSSAINA 179 & 180πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘

Misalin qarfe bakwai na safe hassana ce na hango kwance akan gado se sharar baccinta take,ta rufe jikinta cikin silky blanket purple,gashin kanta ya rufe mata fuska se baccinta kawai take,ta lunkume guri daya da yake dakin ya hade da sanyin qasar da kuma sanyin ac,turo kofar dakin akayi hashim ne ya shigo cikin gajeran wando baqi da rigar shan iska fara,yana shigowa ya mayar da kofar ya rufe tako yake kaman wani barawo daya bayan daya,dede wurin hassana ya tsaye ,yayi tsaye yana qaramata kallo,gefenta ya zauna,ya sunkuyo da kansa dede fuskanta,hannu yasa ya janye mata gashin kanta da ya rufe mata fuskanta,tare da sumbatarta akan goshi,hassana batasan ma anayi ba dan bacci ne mai nauyi ya dauke ta,nan ya hau shafar kanta ahankali ya dauki dan lokaci yana shafar gashin kanta tana bacci…….

Gefen su nabil kuwa duk sun shirya,tsaye yake a harabar gidan wurin shan iska ya goya hannayen sa biyu a bayansa,sanye yake cikin qananun kaya riga yellow wando baqi,ga sumar kanshi tayi lamo lamo se qyalli take,qamshi kawai yake fuskansa dauke da murmushi,cen na hango wata santaleliyar budurwa tana tako daya bayan daya cikin doguwar riga ta qananun kaya yellow,tayi fakin gashin kanta guri daya,seda ta qaraso dede nabil sannan na gane farhana ce ta qara kyau ,ta qara fari ,fatar jikinta kaman ka tabata jini ya fito,se kyalli take,tana isowa gab da nabil bayansa ta tsaya tana qara mashi kallo,ta jima ahakan kaman anyi da shi da ya juya ,yana juyawa sukayi four eyes da farhana,kallon juna suke cikin ido,ko kyabtawa babu da ka gansu kasan tsantsar soyayya ce kawai awurin,lumshe ido farhana tayi tare da maida dubanta a qasa,murmushi yayi yasa hannu ya daga fuskanta sama,cikin murya mai dadin sauraro yace mornin baby,tace morning,rungumota yayi qamqam a kirjinsa tare da lumshe ido,itama farhana rungumesa tayi tanajin bugun zuciyarsa,da yake yafita tsayi sosai,suna cikin haka nabil yace whats wrong?zame jikinta tayi daga nashi ahankali ta rike hannayensa biyu,sannan tace nothing much is just dat am….se tayi shuru ,yace your what ?tace bansan da wane ido zan kalli daddy ba,murmushi yayi yace com on farhana your parents love u so much,daddy kuma he still want to hug u in his arms,sannan ya gayamaki mummy is gone saboda shima kanshi besan tana raye ba,ido ta zaro ta kalli nabil,ya gyada mata kai,yace nima kai na i have no idea mummy ta gayaman,farhana tace i don’t get you,yace alright lets have a walk,tako suke daya bayan daya yana rungume da ita,yayi gyaran murya yace mummy ta gayaman cewa daran da tayi deciding zata bar qasar nigeria daddy besani ba se daran da zata wuce abuja,tana abuja a airport aka sanar dasu cewa jirgin su bazai samu tashi ba saboda problems,nan ta sauka a hotel,tana kwance a hotel takejin labarin cewa ansamu plane crash,wanda mutane da dama sun mutu wasu kuma baa ga gawar tasu ba,labarin yabibiye gari sosai ba wanda be samu wannan labarin ba,so daddy ya dauka mummy tana ciki shiyasa kowa ya dauka cewa mummy is dead,daga ni seke mukasan cewa shes alive sannan tace tayi hakane saboda batasan ta qara jin labarin ki dana daddy,amma kinga  farko da naje she wanted to see you again ,she wanted to hug you,toh kinga inda batason ki ayyi bazata so ta qara ganin ki ba,so da yawa bahaushe kance “hannun ka bazai rube ba kace zaka yanka ka yar ba’ english kuma yana cewa”it is too late to cry wen d head is cutoff”always b loyal to ur parents as long as daddy is concern ni nagayamaki babu abunda yakeso irin ya qara ganin ki,babu abunda yakeso irin ya qara hugging dinki,so kada kidamu kinji,shashshekan kukan da yakeji ne yasa ya tsaya chak sunyi nisa daga gida sosai,ya rungumeta yace banasan naga hawayenki ,kiyi hakuri am always there for you ,i love u so much farhana ,cikin muryan kuka tace i love u too nabil…….

Gefen mummyn ahlam kuwa kicin na tarar da ita tana hada breakfast se sauri take,daddyn ahlam ne ya shigo kicin din tsaye yayi abakin kofa yana kallanta ita kuwa batasan ma da shi ba se aiki take abunta,ganin yanda taketa sauri yasa ya girgiza kai ya fice daga kicin din,dakinsa ya nufo,bayan wucewansa mummyn ahlam ta juyo tace whos there?shurun da taji ne yasa ta dora daga inda ta tsaya,bayan shigar daddyn ahlam a daki safa da marwa ya soma yi ,nazari yake kala kala nisa yayi tare da tsayawa chak yace wai me yake damun hamida ne gaba daya shes not herself, na tambeta taceman nothing but for sure something is wrong ,gaba daya shes confused nd scared i need to no whats going on,juyawa yayi a hasale ya fice daga dakin be taka birki ko ina ba se wurin dinning daya hangota tana jera kayan breakfast tako yayi zuwa wurin yana zuwa hannu yasa yayi mugun jawota seda ta fada akan kirjinsa,cikin takaici tace me haka abban ahlam?idanuwansa sunyi jawur,jikinsa har rawa yake ,yace ke zan tambaya hamida whats going on?kwana biyu na kasa gane kanki i ask u times without number amma sede kawai kice ur fine ur fine,cikin tsawa yace tell me why are u avoiding me,bakida buqata dani ne ko kin samu wanda yafini ne?jin wadannan kalaman suna fitowa daga bakinsa jikinta ya dau rawar hawaye ne ke zuba daga idanuwanta,cikin muryar kuka tace why?what have i done wrong ?dama nasan wannan ranar zata zo,i have been waiting for dix special day,da gudu ta fice daga wurin se dakinta ta shiga kan gado ta fada ta fashe da kuka mai tsuma zuciya sosai take kukan ,tun daga dinning yake jiyo sautin kukanta jikinsa ya mutu sosai,nan da ta barshi anan yake tsaye ya kasa komai ,hannu yasa ya dafe kansa yace ya Allah,cikin hanzari ya juya ya nufi dakin ,kwance ya tarar da ita se kukan take,ya lumshe ido cikin rawar jiki ya nufi gurinta ,gefenta ya zauna hannu yasa ya shafa gashin kanta yace am sorry my hamida is just dat nagaji da ganin ki cikin damuwa nakasa jure ganin ki ahaka ne,na tambe ki kin kasa gayaman ya kike tunanin zanji ne,u no how much i luv u baby please forgive am sorry,kukan taci gaba da yi,cikin muryan kuka tace dama cen baka sona ka aure ni,dama cen kasan bandace dakai ba ka aure ni saboda ka tozarta ni,haba abban ahlam why?dagota yayi daga kwanciyar da take ya rungumeta qamqam a qirjinsa yana lallashinta,ita kuwa se kuka take,yayi dayasanin kalamanda ya furta mata amma shima kanshi ranshi ne ya bace saboda gaba daya ya kasa gane kanta kwana biyu ita kuwa ta kasa gayamasa komai……………

NOTE:SAURIN FUSHI BAYADA KYAU BAGA MA’AURATA BA KAWAI HARGA KAWAYE SABODA ZAKU IYA FURTAWA YAN UWAN KU KALAMANDA BUSU DA CE BA SE DAGA BAYA KU DAWO DA KUNSANI,SHIYASA ANNABI MUHAMMAD S.A.W YAKE YAWAN CEWA “LATABAGADU”KADA KUYI FUSHI ,MU KASANCE MUSULMAI YAN UWAN JUNA .ALLAH YASA MU DACE……AMEEN

Gefen su hashim kuwa koda naje ya shirya tsab cikin kabtan riga da wando milk yayi kyau sosai da kaga dinkin kaga dinkin yan gidan sarauta,ya sa hula baqa takaansa da agogon hannunsa baqaqe ne suma,yayi kyau se kace wani ango se sheki yake da qamshi,tsaye yake a fallo yana qoqarin sa aninin rigarsa,gyaran murya na juyo koda na juya shima hashim ya juyo hassana ce muka gani cikin doguwar riga ta material milk,dinki yasha stone work mai dogon hannu ce pencil hand,se rolling da tayi da black veil itama cikin ta ya qara fitowa ta qara tsufa,amma kullun hassana se kyau take qarawa,wani mayan murmushi ne hashim ya sakammata me tafiya da hankalin duk wani mai karatu ,kunya taji ta maida dubanta qasa,nisa yayi yace har kin fito kenan?ta dafa kai sama ta kalle shi tace eh,mekake yi ne?yace inasan nasa botton din rigana ne na kasa,murmushi tayi tace se kace wani qaramin yaro,bece da ita uffan ba se kallo da ya bita da shi,tako take cikin natsuwa harta qaraso wurinsa ,miqa hannu tayi zuwa rigansa dan tasa masa aninin,hannayensa ya dora akan waits dinta,yana kallanta numfashin su yana suka akan junan su lokaci daya,nan take tasa masa aninin sannan ta banka masa harara cikin so da kaunar juna tace bansan ko yaushe zaka girma ba,murmushi yayi har yanzu hannunsa nakan waist dinta yace as long as u re with me bazan taba girma ba ,hannayenta ta dora akan kafadarsa tare da dora kanta akan kirjinsa,wata ajiyar zuciya tayi mai qarfi tare da lumshe ido wando yasa hashim ya dan ya mutse fuska tare da cewa are you okay?tace yes am fine,shafar bayanta yayi sannan yace are you missing me?tace like crazy,yayi nisa yace i love u so much baby ,tayi murmushi tace love u too,rungume juna sukayiπŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

      πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

               πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

                              πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

 Gefen su nabil da farhana kuwa sun shirya tsab,tsaye suke a fallo suna jiran fitowan mummyn farhana,nabil yana rike da hannun farhana ,tayi rolling da white veil mai ratsin baqi aciki tayi kyau sosai,nabil se satar kallonta yake,gyaran murya tayi tace hayateee?yace naam baby,tace waze kaimu airport din naga bakayi maganan taxi ba sannan time is going,murmushi yayi yace kada kidamu dats not gonna be a problem,tace alright den i trust u,yace really ?ta juyo suna kallon juna cikin ido tace yes,hannu yasa ya shafi fuskanta yace mummy’s little angel,kallon soyayya ta masa tare da daga masa gira,tuntsirewa yayi da dariya ya rungumeta akan kirjinsa,suna cikin haka ,se suka jiyo ana knocking ,nabil ne ya zame jikinsa yace bari na duba,tace okay,tako yayi zuwa kofar gidan yana zuwa ya bude hashim ne tare da hassana,musabaha sukayi da juna sannan yagaisa da hassana tare da tambayar lafiyar jikinta da kuma babynta,tace masa all fine alhamdulillah,shigowa sukayi yana gaba suna biye da shi a baya,fallo suka qarasa inda yake tsaye da farhana,koda yaje farhana ta daga mummynta ce a tsaye tana sa agogon hannu,bayan sun qaraso hashim yakai har qasa yagaita lokaci ne ta dago kanta fuskanta dauke da murmushi tayi tako zuwa wurinsa kafadarsa ta dan dafa ,sannan ta rungume hassana,ta shafi cikin hassana tare da mata fatan sauka lafiya,dukan su suka amsa da Ameen….mummyn farhana ta rungume hassana tare da maida dubanta akan hashim dake gefen hassana,tace tau yanzu kai kuwa twins kakeso ko yan uku?tun before yayi magana hassana tace yan uku mummy tare da zaro ido,dariya suka tuntsire da ita,suna cikin haka se ga farhana ta fito janye da akwati biyu babba da qarama tana fitowa taci karo dasu hashim murmushi tayi tare da cewa manyan baqi mukayi yau?hassana tace wawww farhana kinga wani kyau da kika qara kuwa abun baa cewa komai ma sha Allah,mummy hala me sirrin?hashim ya katse ta  da nabil ne sirrin mana ko kin manta,tayi murmushi tace uhmmm ,tako tayi zuwa wurinsu,musabaha sukayi da ita da hassana,ta dawo gefe suka gaisa da hashim cikin sakin fuska,kaman babu abunda ya taba faru tsakanin su,nabil ne yayi gyaran murya yace kun ku wuce mu tafi na lura idan muka biye maku bazamuje ko ina ba,hashim yace ooooh abun tun yanzu ka bari adaura mana,tuntsirewa sukayi da dariya……………..

         πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

                              πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Hashim da hassana ne suka kai su airport busu dawo ba har sede jirgin su zuwa nigeria ya tashi,bayan fitowar su daga airport busu taka birki ko ina ba se hospital,nan suka zarce se office din doctor ,zaune suka tarar da shi akan kujera se lilo yake,yana latse latse akan computer da take gaban shi,bayan shigowar su suka gaisa,kujera ya nuna musu hassana ce ta zauna hashim yana tsaye abayanta ya dora hannayensa biyu akan kafadarta yana mata tausa,doctor yayi murmushi yace welldone mr hashim,bayan sun gama gaisawa yake tambayarsu ko me yake tafe dasu,hassana ce tayi gyaran murya tace dama sun zo ne saboda suna san su samu wani detail akan wata mace,gyara zaman sa yayi tare da bada dukkan attention dinsa akansu yace wannan kuwa wacece?hashim ne ya amsa da cewa doctor i think she ur patience nan ya hau bashi labarin details din komai tun daga lokacin da ya fara ganinta da kuma dakin da take yawan shiga,doctor ya katse shi tare da daga masa hannu murmushi yayi yace are you talking about maman hamida?cikin hanzari hassana ta daga kanta sama ta dube hashim shima kanshi kallanta yake,hashim yayi saurin cewa yes doctor shes d one we are talking about,doctor yayi murmushi tare da girgiza kai yace tabbas labari ne mai tsawo amma a takaice accident sukayi wanda da kyar aka samu mutane suka rayu tana daya daga cikin mutanen da suka rayu,amma ta samu problem a brain wanda se anfita da ita waje anmata aiki,lokacin babu wanda yasan wacece ita ko daga ina ta fito?temakon da gwamnati takeyi yasa ta samu aka biya mata sannan aka kawota calfonia bayan anmata aikin successful,bayan ta farfado babu sunan da take fadi se hamida ,idan ka tambeta sunan ta se tace mummy hamida,shuru sukayi suna saurarensa….gaba daya labarin da yake basu da turanci yayi sa,abun ya soso ran duk wani mai imani……

MRS NOOR’S NOVELπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

                  πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

HASSANA DA HUSSAINA 177& 178πŸ’ŸπŸ’ŸπŸ’ŸπŸ’ŸπŸ’ŸπŸ’ŸπŸ’ŸπŸ’Ÿ

Hassana na zaune a fallo akan sofa,ta miqe kafafuwanta ,hannunta daya akan cikinta dayan kuma remote a hannun,kallo take wani american film se murmushi take abunta,sanye take cikin doguwar riga yellow ta english wears ta mata kyau sosai,ta qara fitowa da kyaun ta ga cikinta ya fito,tayi fakin gashinta da rubom black ,wayanta ce tayi qara,harta aje kafafunta qasa zata tashi ta dauko wayan ,hashim yace me zakiyi malama?tace wayana zan dauko,harara ya banka mata tare da cewa koma ki zauna,murmushi tayi ta koma kan kujeranda take zaune ta zauna,tako yayi har zuwa inda tasa charge ya cire charge ya dauko mata wayanta,yana zuwa zama yayi gefenta ya zuba mata ido se kallanta yake,murmushi tayi tace wannan kallo fah?yace duk cikin so ne,ta tuntsire da dariya tace sannu baban soyayya,suna cikin haka wayanta ta sake qara wayan na hannun hashim,jin ankira yasa ya duba koda ya duba yaga mummyn ahlam,miqa mata yayi ba tare da yace komai ba,daga wayan tayi bayan ta daga sun gaisa ,mummy ahlam tace tanason taga hassana cikin gaggawa,jin hakan yasa hankalin hassana yayi mugun tashi,miqewa tayi tsaye tace lafiya mummyn ahlam?nisa tayi tace nidai kizo i need your help,bata tsaya jin wata ba tace okay calm down on my way…..

Bayan sun gama wayan hassana tayi tsaye,hashim ya riko hannunta yace lafiya baby?lumshe ido tayi ta gayamashi yanda sukayi da mummy ahlam,hashim yayi nisa yace tau lafiya kuwa?hassana tace i don’t know but she sounds worried,miqewa yayi tsaye yace muje gani koh?batayi masa musu ba nan ta tsaya ya shiga cikin daki ya dauko mata mayafinta da takalmanta ,bayan ya fito ya dora mata mayafinta akai,sannan ya duga ya saka mata takalman ta,murmushi tayi ta ce nagode,ya riko hannunta suka fito,haka ya bude mata mota ta shiga sannan ya rufe ya zagaya gefen mai tuqi,suna kan hanyar su,hassana tace baby?yace yade ,hannun sa ya dora akan nata ya soma shafa shi,tace ya kake ganin zaman farhana da nabil ze kasance ne?hashim yace meyasa kikayi magana?hassana tace saboda tana nuna man cewa bazata iya zaman aure da shi ba saboda abubuwan da ta aikata shes shy nd nervous,hashim yace Allah sarki nabil kuwa yana sonta sosai,saboda gaba daya baya ganin laifin da ta aikata kullun cikin yabonta yake da gayaman yanda yakesonta,hassama tayi nisa tace Allah ya kyauta,haka yaketa janta fira har suka isa gidan mummy ahlam,zaune take a fallo ta zuba wani uban tagumi tayi nisa a tunanin da take,hassana ce ta shigo tare da sallama amma taji shuru,jin shurun yasa ta qaraso cikin fallo ita a tunaninta mummyn ahlam tana ciki,har zaya qara wata magana taga mummyn ahlam zaune a fallo,tsayawa tayi chak tana qara mata kallo,ganin tayi nisa a tunanin da take yasa hassana ta dafa kafadarta da sauri ta daga kanta sama,ido biyu sukayi da mummyn ahlam,murmushi tayi tace yaushe kika qaraso?hassana tace nadan jima anan tsaye,me kike tunani ne haka?murmushi tayi tace da hassana yar uwa zauna,batayi musu ba ta zauna,ajiyan zuciha tayi tace idan baki manta ba na taba baki labarin cewa i lost my parents in an accident koh?hassana tace yes,mummyn ahlam tace yawwa before a sallame ki naje hospital din,na tarar da kina bacci dake da hanan,se na fito bayan na fito na hadu da wata mata exactly yanda kikaga mummyna haka take,amma abunda bangane ba shine ta wuce na wuce amma bata ganeni ba,shine nakesan na tambeki ko kin taba ganinta?hassana tace kina da hoton ta,mummy ahlam tace bari nazo miqewa tayi ta nufi cikin daki,bayan yan mintuna ta fito rike da wani hoto a hannunta,data qaraso seta miqawa hassana tabbas itace matar da su hanna da hanan ke zuwa gurinta hospital inji ni mrs noor,hassana tace no gaskiya bansan ta ba,amma meyasa baki bita bane?mummy ahlam tace bansan room dinda ta shiga ba sannan banida tabbas ko ita ce aka kawo ko kuma kama ce kawai,hassana tace yes it can be possible but inaga idan aka tambaya ko muka qara ganinta zamu gane komai………….πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Mummy ahlam tace hakane kuma,but seriously  ni inaji ajikina cewa shes my mum,saboda koda muka rabu da ita inada shekara goma sha bakwai a duniya,but angayaman sun mutu saboda baa ga gawar su ba motan tayi qurumus,den taya wannan dana gani zata zama mamana?hassana tayi murmushi tace ya kike magana kaman bakisan ikon Allah ba ,ba mamaki itace mahaifiyar ki sannan ba mamaki iyayen ki da ransu,everything is possible ,nothing is impossible so please ,mummy ahlam tace toh what do you think we can do now?hassana tace meze hana nagayawa hashim may b baze rasa sanin ta ba ko ganinta a hospital tunda all d time yana cen,mummyn ahlam tace ooooh shiya kawo ki?hassana tace eh,mummyn ahlam tace bakida kirki shine kika bar shi waje,hassana tace aaaah not my fault ayyi gidan ba baqonsa bane,wayanta dake hannunta ta dauka ta dannawa hashim kira tace da shi daya shigo,be dauki wani dogon lokaci ba se gashi cikin gidan,bayan sun gaisa wuri ya samu ya zauna,hassana ta gayamasa komai,yace naga hoton,hassana ta miqa masa,ido ya zaro yace i know her very well,mummy ahlam ta miqe tsaye tace where? please hashim help me i need to see her yayi murmushi yace sit down nd calm down okay,ayyi koda yaushe su hanna da hanan na gurinta har hajia tasanta,saboda dasun zo cen suke zuwa suyi zaman su,sun shaqu da ita nesa ba  kusa ba,nisa yayi yace yanzu mummy ahlam yaushe kikeson zuwa nakai ki gurinta?mummyn ahlam gaba daya ta riki ce ta fita hayyacinta ,cikin rawar murya tace ko yanzu ashirye nake hashim i really need to see her,yace alright den wannan bakomai bane,amma kinga yanzu dare yayi meze hana ki bari gobe da safe muje i promise zanzo nakai ki har dakinda take,nan mummyn ahlam ta hau yiwa hashim godiya,hassana tayi murmushi tace u deserve more than dix kada kidamu am sure shes your mum,mummyn ahlam tace i hope so nd i pray so,hassana tace ki kwantar da hankalin ki komai ze dawo normal❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀❀

Busu jima ba agidan suka fito rakiya tayo musu har wurin parking space,nan sukayi seda safe suka wuce ta koma cikin gida,nan ta hau safa da marwa a fallo,ta dauki lokaci mai tsawo tana safa da marwa cen ta tsaya chak dubanta ta maida kan agogon bangon da ke fallon taga misalin qarfe takwas na dare,nisa tayi tare da lumshe ido tace yanzun nan daddyn ahlam ze dawo da yaransa zama be sameni gashi ko girki ban dora ba,hanyar kicin ta miqe ta shiga nan ta hau qoqarin dora girki,macroni ce zata dafa da kifin gwango…gefen su hashim da hassana kuwa straight macdonald suka faka hashim ya shiga ya siyo musu abinci da snacks da ice cream bejima ba ya fito gida suka dawo straight,falo hassana ta zauna a qasa kan carfet ta bude kafafu bayan shigowar hashim dauke yake da ledodin macdonald murmushi yayi yace madam mekike a qasa?tace nan nake sha’awar zama tako yayi ya qaraso zuwa gareta yace tabbas baby boy dina sarkin kansa ne,hassana ta turo baki tace sarki mai wahalda mahaifiyarsa,ayyi idan ya fito se ya sha duka,hashim ya nufi kicin yana fadin Allah kema ki sha duka,batace masa komai ba se jinginawa da tayi akan sofa tare da lumshe ido,jin tayi shuru ne yasa hashim ya fito ya duba lafiya,cikin hanzari ya qaraso gurinta cikin sanyin murya yace lafiya babyna?tace bakomai ba tare da ta bude ido ba,zauna yakai shima ya janyota ya kwantar da ita akan kafafunsa miqe kafafunta tayi tana maida numfashi sama sama,shafar kanta ya soma yi yana hura mata iska daga bakinsa,wayansa ce tayi qara hannu yasa a aljihun wandon ya dauko,mummynsa ce ke kiransa da sauri ya daga bayan sun gaisa take tambaya ina babynta(hassana)?ya gayamata abunda ya faru,tace ka bata ruwa masu sanyi tasha tun before nabar garin nagayamaka yanzu take bukatar kulawa fiye da tunaninka,fada ta hau masa se hakuri yake bata,bata jira mezece ba ta katse wayan,yayi murmushi ya juya ya dauko fillon sofa ya dora kan hassana a sama ya shiga kicin ya dauko gorar ruwa mai sanyi da cup,yana zuwa ya zuba ruwan a cup ya tada hassana ya bata,shan ruwan take kaman wadda tayi shekara bataga ruwa ba,shima kansa abun ya bashi mamaki ,be taba ganin tasha ruwa haka ba,bayan ta gama ya dauketa kaman baby ya shiga da ita daki kan gado ya kwantar da ita,kanta ya soma shafawa ahankali bacci ne ya dauke,ido ya zuba mata se kallanta yake,ganin bacci mai nauyi ya dauketa,ya jawo bargo ya rufeta,ya fice daga dakin,fallo ya dawo ya zauna,abincin da suka siyo da snacks,ya dauki ledodin ya shiga dasu kicin fridge ya bude gaba daya ya cire su cikin leda yasa a fridge,cake daya ya bari se ice cream daya,ya dauko gorar ruwa daya,dora su yayi akan tray ya fito dasu fallo yazo ya zauna akan sofa,nan ya soma cin cake dinsa da ice cream bayan ya gama yasha ruwa,kwantawa yayi akan sofa ya miqe kafafuwansa kansa a sama yana kallan sili,wayansa ce tayi qara,da sauri ya tashi zaune,kan centre table take koda ya duba nabil ne ke kiransa,murmushi yayi ya daga bayan ya daga suka gaisa,nabil ne yace aboki gobe fah zamu koma nigeria,hashim yace kai haba?nabil yace in sha Allahu,yanzu haka maganar da nake maka nayi mana booking komai,hashim yayi murmushi yace ma sha Allahu ,Allah ya kai mana rai ,wane time zaku je airport?nabil yace around 12,hashim yace okay den babu matsala se nazo munyi bankwana kenan?nabil yace sosai ma ,ina madam?hashim yace tana bacci,yace baby fah?hashim yace shima yayi bacci,nabil yace ka gaida man dasu,hashim yace ka gaida su mama,sukayi seda safe da juna, hashim yayi murmushi yace wani iko se Allah,dama ance komai yayi farko zeyi qarshe,yanzu farhana is getting married to nabil,tabbas hassana tayi gaskiya duk inda kaga mutun ka nema mishi shiryuwa awurin ubangiji bawai ka zage shi ba,sbd kaima bakasan qarshen ka ba,i luv u so much hassana,jin yayi ance i luv u too hashim,da sauri ya juya ido biyu sukayi da juna hassana na jingine akan kofar dakin taci ado cikin wasu kayan bacci masu daukar hankali,riga ce guntuwa pink,sharashara kana ganin jikinta,ga cikinta ya fito ,ta zubo gashin kanta har gadon baya,se sheqi take da qamshi,murmushi ta sakammasa mai dauke da alamar tambaya hashim gaba daya dauke wuta yayi saboda ya kasa komai se kallanta da yake,tako tayi zuwa wurin shi,gab da shi ta zauna tare da lumshe ido,ta bude cikin murya mai dadin sauraro tace ya akayi abban yara?ajiyan zuciya yayi mai qarfi sannan yace komai ma anyi wannan wanka haka,murmushi tayi tace wanka be maka bane?qara matsowa yayi ya rungume abarsa,yace baa cewa komai,tayi murmushi tace abban yara?yace naam my baby,nisa tayi tace i need a favor from u,yace wace iri anything for my queen,kanta ta daga ta dube shi cikin ido tace dubai nakesan na haifi babyna……

Bece da ita komai ba se kallan juna da suke cikin ido,hannu yasa ya shafi fuskanta sannan yace is not possible,ya mutse fuska tayi tare da turo masa baki,ido ya fiddo yace tsaya kin fah san komai nan kikeyin sa ,taya zan kai ki dubai ki haihu?com on baby ki bari ki haihu anan idan kika qara samun wani se muje daga nan har qasar sin,alamar kuka ta fara mashi cikin shagwaba take fadin Allah ni bazan haihu nan ba,dubai nake so,harda hawaye,cumuimuye shi tayi guri daya ta rike masa riga,dariya ya tuntsire da ita yace alright naji zaki haihu dubai din,is dat okay?ta gyada masa kai tare da murmushi,hannu yasa ya goge mata dan guntun hawayen ta,cen tace masa yunwa takeji,miqewa yayi ya shiga kicin ya dauko mata pizza,cake,ice cream da ruwa kan faranti ya dora su,yana zuwa ya zauna ya dora farantin akan kafafunsa,nan ya soma feeding dinta ahankali se tsokanar ta yake…….suna cikin haka yake bata labarin kiran da nabil ya masa,tace ayya am so happy for them but abban yara anya farhana zata amince ta auri nabil kuwa?hashim yace kidaina fadin haka mana meyasa bazata amince ta aure shi ba?mutunen da ya maka haka ayyi inaga ya gama maka komai,hassana tayi nisa tace alright den,gobe zamu kai su airport?yace eh haka nake tunani daga cen se mu wuce hospital yin aikin maman ahlam,hassana tace okay den.haka sukaci gaba da soyayyar su cikin natsuwa da kwanciyar hankaliπŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

 ****NIGERIA****mummy mashkura ce zaune akan doguwar sofa fara dake makeken fallon ta mai dauke da kayan ado na sarauta dana ado,dsanye take cikin doguwar riga jallabiya baqa se mayafin rigar da ta yafa baqi,kafa daya ta dora akan daya,fuskanta bako annuri se lumshe ido take tana kyabci,turo kofar fallon akayi ahankali jekadiya ce cikin atamfa riga da zane,tana sanye da dogon hijabi baqi,sallama tayi ta qaraso,tana shigowa qasa ta zube tana kai gaisuwa zuwa ga sarauniya mashkura,dubanta ta maida kan jekadiya tace barka da zuwa jekadiya,jekadiya tace ranki shi dade lafiya kuwa?naga ranki a bace,cikin hasala tace ina kuwa lafiya jekadiya yarima baya kula da hassana ko daga nan zuwa cen,shiyasa banso aka barshi tare da ita ba ,gashi ciki ne da ita wanda likita ya tabbatar man da cewa babu abunda take buqata irin kulawa,murmushi jekadiya tayi ta sunkuyar da kanta qasa tace Allah ya huci zuciyarki sarauniya,kinsan halin yaran zamani dole se kin hada da hakuri,ajiyan zuciya tayi mai qarfi sannan tace hakane jekadiya amma dai sakacinsa yayi yawa wallahi banasan abunda zai tabaman ita ko daga nan zuwa cen,jekadiya tace hakuri zakiyi,sarauniya mashkura tayi murmushi tace ayyi dole tare da yarfa hannu,sannan tace yawwa jekadiya lafiya naganki da rana tsakiya?jekadiya tayi gyaran zama tare da gyaran murya tace wallahi ranki shi dade matar dana ce a asibiti zata haihu amma babu kudi,sarauniya mashkura tace me hadin haihuwa da kudi?jekadiya tace aiki zaa mata saboda ta kasa haihuwa da kanta,sarauniya mashkura ta gyada kai tace Allah ya sauketa lafiya kaman nawa ake buqata?jekadiya tace tau ranki shi dade sunce dubu hamsin ne,sarauniya mashkura tayi nisa tace tau zan baki dubu dari saboda kada a bukaci na magani kizo baki sameni ba,jekadiya ta dora yiwa sarauniya mashkura godiya tana mata addu’oi daban daban na alhairi,dubanta sarauniya mashkura ta maida gefenta,wayanta ta dauka ta dannawa hidaya kira,bayan ta daga tace ki bani 100k a safe ,seta katse,bayan ta gama tace gaskiya jekadiya idan zuwaira ta haifi wannan lafiya ta bari ta huta naga haihu tana bata wahala,jekadiya tace wallahi hakane dan ko haihuwar habu haka akayi,sarauniya mashkura tace Allah sarki kowa da irin tashi suna cikin haka suka jiyo sallama,hidaya ce ta shigo rike da kudi ahannunta sanye take cikin riga da sket na atamfa,tayi fakin gashin kanta ko kwalliya batayi ba amma se kyalli take,tana qarasowa ta gaida jekadiya murmushi tayi tace gimbiya sannu da fitowa,hidaya tace mummy ga kudin,sarauniya mashkura tace ki bawa jekadiya miqawa jekadiya tayi hannu biyu jekadiya ta saka ta karba se godiya take yiwa sarauniya mashkura,sarauniya mashkura tace bakomai jeki ,miqewa tayi tare da musu fatan alhairi,sarauniya mashkura tayi murmushi,bayan fitar jekadiya gefen mummy mashkura hidaya ta zauna……

Ta shige jikinta kaman wata mage,murmushi mummy mashkura tayi ta rungume hidaya qamqam,tace ya akayi amaryar adnan?murmushi hidaya tayi tace mummyna?mummy mashkura tace naam hidayana,tace i love you so much Allah banason abunda zai rabani dake,ajiyan zuciya mummy mashkura tayi tace hakane hidayana nima banasan abunda zai rabani da yarana ko daga nan zuwa cen,amma ya zama dole mu rabu saboda ku mata ne zakuyi aure kuje gidajen wasu ,yarima ne kawai zai kasance tare dani se idan kunzo ganina,fatana daya adnan ya rike man ke amana,ya baki kulawa ta musamman ya kula da addinin ki,ya kuma girmamaki amatsayin ki na matarsa,saboda nan da yan watanni zaki barni kije gidan mijinki se kuma idan kinzo ganin gida ko munyi waya before you no abubuwa sun maki yawa idan kin kai da kids by den u will b very busy☺☺☺☺☺☺☺,fashewa da kuka hidaya tayi mai tsuma zuciya ,jin kukan yasa mummy mashkura tace kai kuka kike?com on baby is okay,rungume ta hidaya tayi qamqam cikin rawar murya take fadin i luv u so much mummy can’t do without kada ki bari adnan ya kwacemaki ni,dariya ta tun tsire da ita tace tau ya isa shafar bayan hidaya take tana lallashinta,hidaya se kuka take sosai,mummy mashkura gaba daya jikinta yayi sanyi,itama kanta qarfin zuciyarta kawai tayi  amma harda hawaye seda tayi,bata san abunda zai rabata da yaranta amma yanzu ya zama dole saboda aure zasuyi…….haka suka kasance aranar 😣😣😣😣😣😣😣😣😣😣😣😣😣😣😣😣😣😣se ka rantse ranar zaa kai ta dakin adnanπŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…

   MRS NOOR’S NOVELπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž